Tinubu ya ba da umarnin ceto ɗaliban Gusau

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa hukumomin tsaro umarni kan su gaggauta ceto ragowar ɗalibai mata na jam’iyyar tarayya da ke Gusau waɗanda ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su kwanan nan.

Idan ba a manta ba, a ranar Juma’ar da ta gabata wasu ‘yan bindiga suka bi ɗaliban har ɗakunan kwanasu suka sace su.

Sa’o’i kaɗan da faruwar lamarin rundunar tsaro ta haɗin gwiwa, wato Hadarin Daji, mai yaƙi da matsalolin tsaro a yankin, suka samu nasarar kuɓutar da mutum shida daga cikin ɗaliban da aka yi awon gaba da su.

Umarnin na Tinubu na ƙunshe ne cikin sanarwar da fadar shugaban ƙasa ta fitar a ranar Lahadi.

Shugaban ya jaddada ƙudurin gwamnatinsa na kare ran kowane ɗan ƙasa, tare da bai wa iyayen ɗaliban da lamarin ya shafa tabbacin ceto ‘ya’yansu cikin ƙoshin lafiya.