Daga BASHIR ISAH
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa wani kwamiti na musamman wanda zai maye gurbin hukumomin gudanarwa da aka sauke a makon jiya a ɗaukacin ma’aikatun Gwamnatin Tarayya kafin a naɗa wasu sabbi.
Majiyarmu ta rawaito cewa, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, wato Hon. Femi Gbajabiamila, shi ne wanda Tinubu yaɗa shugabancin kwamitin.
Ta ce aikin kwamitin shi ne zaɓowa da kuma tantance waɗanda za a naɗa hukumomin gudanarwa a ma’aikatun da lamarin ya shafa daidai da tsarin gwamnati.
Haka nan, wata majiyar daga Fadar Shugaba Ƙasa ta bayyana cewa, Shugaba Tinubu ya ƙalubalanci kwamitin da ya tabbatar ya yi aiki mai tsafta tare da fahimtar yanayin kowace ma’aikata domin sanin waɗanda suka cancanta a naɗa jagorancin.
Majiyar ta ce an kuma buƙaci kwamitin da ya yi la’akari da sassan ƙasa baki ɗaya yayin zaɓo waɗanda za a naɗa a hukumomin.
Mambobin kwamitin sun haɗa da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Hon. Femi Gbajabiamila, Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume da Mai Bai wa Shugaban Ƙasar Shawara na Musamman Kan Sha’anin Siyasa da Harkokin Gwamnati, Malam Yau Darazo da sauransu.