Tinubu ya buƙaci gwamnonin Arewa ta tsakiya su kasance tsinsiya baɗaurinki guda DAGA JOHN D. WADA, a Lafiya

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙalubalanci masu ruwa da tsaki da duka mambobin jam’iyyarsu ta APC maici a yankin Arewa ta tsakiya a ƙasar nan su tabbatar sun ci gaba da kasancewa tsintsiya maɗaurinki ɗaya.

Wannan kiran haɗin kai Shugaban Ƙasar ya yi ne a lokacin wani gagarumin taron masu ruwa-da-tsakin jam’iyyar APC ɗin a Arewa ta tsakiya wanda aka gudanar a birnin Lafiya, fadar gwamnatin jihar Nasarawa.

Shugaba Tinubu wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya wakilce shi a wajen taron, ya jaddada mahimmancin haɗin kai don cigaban jam’iyyar ta APC da ma ƙasa baki ɗaya.

Ya kuma yaba wa jam’iyyar a shiyar Arewa ta tsakiya musamman gwamnonin yankin dangane da aiwatar da ingantattun ayyukan cigaba wa al’ummomin su kawo yanzu inda ya buƙace su da su ci gaba da haɗa kai da gwamatinsa don samun nasarori a fannoni daban-daban.

Haka nan, ya yi amfani da damar inda ya yi alƙawarin ci gaba da samar da abubuwan more rayuwa wa shiyar da ma ƙasa baki ɗaya kamar yadda ya yi alƙawari a lokacin yaƙin neman zaɓen sa don inganta rayuwar al’ummar Nijeriya baki ɗaya.

A nasa ɓangaren, shugaban jam’iyyar ta APC na ƙasa, Dokta Umar Ganduje, ya bayyana wasu sabbin tsare-tsare da jam’iyyar ta fito da su a ƙarƙashin jagorancin sa kawo yanzu musamman na yin rajistar zama ɗan jam’iyyar ta yanar gizo da sauran su inda shi ma ya yaba wa hangen nesa da ‘yan jam’iyyar daga shiyar ta Arewa ta tsakiya suka yi na ƙirƙiro tare da aiwatar da taron wanda ya bayyaa a matsayin mai matuƙar mahimmanci da zai je nesa wajen haɗa kan mambobin baki ɗaya.
 
Haka su ma da suke jawabi a mabambantan lokuta, gwamnonin shiyyar ta Arewa ta tsakiya da suka haɗa da na Kwara da jihar Nasarawa da Kogi da Kaduna da Filato da Binuwai da tsohon shugaban jam’iyyar APC ɗin na ƙasa Sanata Abdullahi Adamu da sauran su.

Duk sun bayyana cewa taron wanda ke da manufar tatttauna tare da haɗa kawunan duka masu ruwa-da-tsakin jam’iyyar na yankin ba shakka ya cancanta kuma suka buƙaci a cigaba da gudanar da ire-iren sa a-kai-a-kai don cimma burin a ƙarshe.