Tinubu ya doke Atiku a Kwara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

An bayyana ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka gudanar ranar Asabar a ƙananan hukumomi 16 na Jihar Kwara.

Tinubu ya samu ƙuri’u 263,572 inda ya kayar da abokin hamayyarsa kuma ɗan takarar Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, wanda ya zo na biyu da ƙuri’u 136,909.

Adadin waɗanda suka yi rajistar zaven ya kai 1,695,928 yayin da waxianda aka tantance suka kasance 497,519.

Jimillar quri’u masu inganci da aka kaɗa 469,971; Waɗanda aka watsar 26,712 sai jimillar ƙuri’un sa aka kaɗa 496,683.

Peter Obi na Jam’iyyar Labour (LP) ya samu ƙuri’u 31,166 ya zo na uku yayin da Rabi’u Musa Kwankwaso na Jam’iyyar NNPP ya samu ƙuri’u 3,141 na ƙuri’un da aka kaɗa a jihar.

Farfesa Paul Annune daga Jami’ar Joseph Sarwuan Tarka, Makurdi (Tsohuwar Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya), shi ne jami’in tattara sakamako na Kwara.

Ƙananan hukumomi goma sha shida da suka haɗa da Ilorin ta Yamma, Ilorin ta Gabas, Ilorin ta Kudu, Asa, Moro, Kaiama, Patigi da Baruteen.