Tinubu ya faɗaɗa shirin ƙarin albashi na N25,000 zuwa ga dukkan ma’aikata

Gwamnatin Tarayya ta faɗaɗa aniyarta ta ƙarin albashi da N25,000 ya shafi dukkan rukunin ma’aikata

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, shi ne ya bayyana haka yayin taron da suka yi da ƙungiyoyin ƙwadago da yammacin Lahadi.

Da fari, ƙarin albashin da gwamnatin ta ce za ta yi ya keɓanta ne ga ƙananan ma’aikata kamar yadda aka ji Shugaba Bola Tinubu ya furta a jawabinsa ga ‘yan ƙasa a ranar bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kan ƙasa.

Tinubu ya ɗauki matakin yi wa ma’aikata ƙarin albashin ne domin rage musu raɗaɗin cire tallafin mai da kuma daƙile yunƙurin tafiya yajin aikin da ƙungiyar ƙwadago ta yi.