Tinubu ya isa Abuja bayan shafe makonni biyu a ƙetare

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya isa Abuja daga tafiyar mako biyu da ya yi zuwa ƙetare.

MANHAJA ya tattaro cewar, Tinubu ya isa fadar Villa da ke Abuja da safiyar Laraba.

A ranar 23 ga Afrilu Tinubu ya bar Nijeriya zuwa ƙasar Netherlands don halartar taron tattalin arziki.

Bayan taron yini uku da ya halarta a ƙasa ta Netherlands, daga nan ya cilla zuwa Saudiyya domin halartar babban taro na duniya kan tattalin arziki, wato WEF a taƙaice.

Sai dai, babu wani bayani a hukumance dangane da tsawaita zaman da Tinubu ya yi a ƙetare, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakamin ‘yan Nijeriya.