Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, ya koma masaukin baƙi na tsaro da ke yankin Maitama a Abuja, da zama.
Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na Tinubu, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan ta hanyar wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Tiwita a ranar Laraba.
A cewar Onanuga, Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima, za su ci gaba da zama a nan masaukin har zuwa lokacin da za a rantsar da su a matsayin Shugaban Ƙasa da Mataimaki a ranar 29 ga Mayu, 2023.
A ranar Litinin Tinubu ya dawo Nijeriya bayan hutun wata guda da ya sha a Turai.
Ga BIDIYON tafiya masaukin: