Tinubu ya lashe akwatin zaɓen el-Rufai a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi nasara a rumfar zaɓen gwamna Nasir el-Rufai na Jihar Kaduna.

Tinubu ya samu ƙuri’u 173 a rumfar zaɓe mai lamba 024, Ward 07, Ungwan Sarki, Kaduna, inda ya doke ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, wanda ya samu ƙuri’u 134.

Peter Obi na jam’iyyar Labour Party LP ya samu ƙuri’u uku, yayin da Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP ya samu ƙuri’u 20.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *