Tinubu ya lashe zaɓen ƙananan hukumomi 6, Atiku ya samu 2 a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya samu nasarar lashe zaɓen ƙananan hukumomi 6 daga cikin 8 da aka tattara kawo yanzu

Babban jami’in tattara sakamakon zaɓe a jihar farfesa Mu’azu Abubakar Gusau ne ya sanar da hakan yau lahadi

Ƙananan hukumomin da ɗan takarar jam’iyyar APC ɗin ya lashe sun haɗa da Matazu, Kaita, Musawa, Ingawa, Charachi da kuma Dutsi sai dai jam’iyyar PDP ce ta lashe zaɓen ƙaramar hukumar Batsari da kuma Kurfi

A babban zaɓen da aka gudanar ranar Asabar.

Tinubu ya samu ƙuri’a 82,332 a faɗin ƙananan hukumomi shidda da ya samu ya zuwa yanzu.

Abokin hamayyar sa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya samu ƙuri’u 69,175, yayin da Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar NNPP ya zo bayansa da ƙuri’u 8,629.

Kwamishinan hukumar zaɓen a Katsina farfesa Yahaya Ibrahim Maƙarfi ya yi godiya ga duk waɗanda suka taimaka wajen samun nasarar gudanar da zaɓen

Wakilan jam’iyyun siyasa daban daban da ƙungiyoyin fararen hula da kuma masu sa’ido kan zaɓe ne suka halarci rumfar tattara sakamakon zaɓen

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *