Tinubu ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa

*Yau za a miƙa masa takardar shaida

Daga BASHIR ISAH

Ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya zama sabon zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Nijeriya.

Tinubu ya yaki wannan matsayi me biyo bayan zaɓaɓɓen da aka gudanar a ƙasar ran Asabar da ta gabata.

Yau Laraba ake sa ran Hukumar INEC za ta miƙa wa Tinubu shaidar lashe zaɓaɓen da ya yi.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, shi ne ha ba da sanarwar nasarar da Tinubu ya samu, tare da cewa za a miƙa masa shaidar ne da misalin ƙarfe 3 na ranar a Babban Zauren Taro na Ƙasa da Ƙasa da ke Abuja.

Tinubu ya lashe zaɓen ne da ƙuri’u 8,794,726, yayin da Atiku Abubakar (PDP) ke bi masa da ƙuri’u
6,984,520, sai Peter Obi (LP) da ƙuri’u 6,101,533, sannan Rabiu Musa Kwankwaso (NNPP) da ya tsira da ƙuri’u 1,496,687.