Tinubu ya miƙa wa Buhari hannayen amsar mulki

*Tinubu ya bada sunayen mutane 13
*Buhari ya ɓaro manyan ayyukan Naira tiriliyan 1.535
*Buhari zai gadar wa Tinubu shirin maganta matsalar tsaro na shekara biyar

Daga SANI AHMAD GIWa da MAHDI M. MUHAMMAD

Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Nijeriya mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu ya miƙa wa Sakataren Gwamnatin Tarayya Mr. Boss Mustapha sunayen mutane 13 da za su yi aiki da kwamitin miƙa mulki da bangaren gwamnati mai barin gado da take ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.

Tinubu ya kasance a ranar 1 ga Maris, 2023, aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu bayan ya doke Atiku Abubukar na Jam’iyyar PDP, Peter Obi na Jam’iyyar Labour, da sauransu.

Ana sa ran za a rantsar da tsohon gwamnan jihar Legas a matsayin Shugaban Nijeriya don maye gurbin Muhammadu Buhari wanda aka rantsar a ranar 29 ga Mayu, 2015 kuma zai cika wa’adinsa na biyu na shekaru takwas a ranar 29 ga Mayu, 2023.

A cikin wasiƙar da aka miƙa wa Boss Mustapha, Tinubu ya bayyana tsohon Sanata mai wakiltar Borno ta Arewa kuma Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa (Arewa) a halin yanzu, Mista Abubakar Kyari a matsayin kodineta kuma daraktan kuɗi da kasafin Kuɗin kwamitin.

Babban Darakta (Cigaban Kasuwanci) a bankin shigo da kayayyaki na Nijeriya (NEXIM), Hon. Stella Okotete za ta yi aiki a matsayin shugabar sakatariya, tsare-tsare da sa ido yayin da Mista Makinde Araoye, tsohon ɗan takarar gwamna a jam’iyyar All Progressives Congress daga jihar Ekiti zai kasance daraktan wurin taro da fareti da kuma rantsar da shi na tsawon mako guda.

Buhari ya varo manyan ayyuka gabanin tafiyarsa:

Ita kuwa Majalisar Zartaswa ta Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta amince da Naira tiriliyan 1.535, domin ginawa da kuma gyara tituna 11 a faɗin ƙasar nan a ƙarkashin tsarin bayar da haraji na Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), duk da cewa, amincewar ta zo ne makonni gabanin ƙarewar gwamnatin.

Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya ce za a kashe kuɗaɗen ne a wasu manyan tituna a Nijeriya, wanda ya kai sama da kilomita 700.

Wannan na zuwa ne kwanaki 40 da cikar wa’adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari na biyu.

Fashola ya ce hanyoyin da za a kammalasu nan ba da daɗewa ba za su haɗe jihohi 11.

Ya lissafa jihohin da suka amfana da suka haɗa da Edo, Delta, Kano, Kaduna, Borno da Adamawa da dai sauransu.

“Majalisar ta amince da gina tare da gyara hanyoyi 11 da adadinsu ya kai kilomita 737.242 a kan kuɗi N1, 535, 154, 247, 234.48 a ƙarƙashin kashi na biyu na tsarin karɓar harajin NNPC.

“Ku tuna cewa a watan Janairun wannan shekara, majalisar ta amince da wata takarda ga NNPC na zuba jarin Naira tiriliyan 1.9 a kan hanyoyin mu. Wannan adadin ya kasance kusan tituna 44 da aka bayar da kuma ma’auni na hanyoyin da sai da aka yi sayayya tsakanin wancan lokaci zuwa yanzu su ne guda 11 da majalisar ta amince da su a yanzu,” inji Fashola.

Gwamnatin Buhari ta ƙaddamar da shirin shekaru biyar na magance matsalar tsaro:

A wani cigaban kuma, Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, a ranar Talata, ya ƙaddamar da wani shiri na tsawon shekaru biyar ga ma’aikatar da ayyukanta don magance matsalar rashin tsaro da ya addabi Nijeriya.

A wata sanarwa da Kakakin Ma’aikatar, Afonja Fatai Ajibola ya fitar, Ministan ya ce, ma’aikatar harkokin cikin gida na da rawar takawa ga tsaron ƙasa da cigaban ƙasar.

Ya ce, ana za a yin waɗannan ta hanyoyi guda huɗu, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) da ke sa ido kan shigowa da fita a kan iyakokin ƙasar nan, tare da tabbatar da cewa an lura da waɗanda za su iya cutar da ’yan Nijeriya da jin daɗin su daga waje.

Ministan ya ci gaba da cewa, hukumar NSCDC, tana bai wa ’yan sanda da sauran jami’an tsaro haɗin kai wajen yaai da miyagun laifuka da tattara bayanan sirri, yayin da hukumar Gidan Gyaran Hali (NCoS) ke tsare da wazanda aka yanke musu hukunci bisa ƙa’ida ko kuma suna jiran shari’a.

Yayin da yake lissafta rawar da jami’an tsaro ke takawa wajen tabbatar da tsaron ƙasa, Ministan ya kuma ce hukumar kashe gobara ta tarayya (FFS) tana bada agajin gaggawa ga gobara da sauran abubuwan gaggawa sannan, ya ƙara da cewa wani sashe a ma’aikatar na yin rijistar aure da kuma tsara kasancewar baki a Nijeriya.

Ministan wanda ya yarda da cewa har yanzu akwai ƙalubalen tsaro, ya bayyana cewa, dubban shari’o’in da a da za su jefa al’ummar ƙasar cikin ruɗani ana magance su a kullum.

Tun da farko a nasa jawabin, Babban Sakataren Ma’aikatar, Dakta Shu’aib Belgore ya bayyana cewa, bayanai da ake da su sun nuna cewa ma’aikatar harkokin cikin gida ta gudanar da ayyukanta ba tare da wani shiri ba har zuwa yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *