Tinubu ya miƙa wuya: Ya umarci majalisa da Ma’aikatar Sharia su yi duba ga sabon ƙudirin haraji

Daga USMAN KAROFI

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ma’aikatar Shari’a ta tarayya da Majalisar Dokoki ta Ƙasa da su duba ƙorafe-ƙorafe da ake yi kan sabbin ƙudirorin gyaran haraji da ya gabatar wa majalisa. Wannan ya biyo bayan suka da cece-kuce da ƙudirorin suka jawo, musamman daga wasu gwamnonin jihohi, inda daga yankin Arewa ake samun mafi yawan adawa.

Wasu daga cikin masu sukar ƙudirorin sun bayyana cewa dokokin na da illa ga yankin Arewa, yayin da wasu ke cewa za su ƙara jefa ‘yan Nijeriya cikin talauci. Don magance wannan matsalar, Shugaba Tinubu ya umarci Ma’aikatar Shari’a ta yi aiki tare da shugabannin Majalisar Dokoki don yin gyaran fuska a ƙudirorin kafin a amince da su.

Ministan watsa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya ce gwamnati ba ta da wani shiri na sirri da zai sa a gaggauta bin tsarin da ba a tantance ba. Ya ƙara da cewa, “Gwamnatin Tarayya na maraba da duk wani shawara mai ma’ana da za ta taimaka wajen magance matsalolin da ake ganin suna cikin ƙudirorin.”

Ya bayyana cewa Shugaba Tinubu na jajircewa wajen tabbatar da gaskiya da biyayya ga ‘yan Nijeriya, yana mai cewa tattaunawar da ake yi kan ƙudirorin alama ce ta kyakkyawan tsarin dimukraɗiya. Ministan ya ce: “Duk da cewa an samu maganganu masu tsauri da wasu zarge-zargen ƙarya, yana da matuƙar muhimmanci a kauce wa kiran sunaye ko saka batutuwan ƙabilanci a cikin wannan muhimmin batu na ƙasa.”

Har ila yau, ministan ya musanta zarge-zargen cewa ƙudirorin na nufin tauye wasu jihohi ko talauta al’ummar ƙasa, yana mai kiran su da “labaran ƙarya ” da “yaɗa bayanan da ba su da tushe.” Ya ce gwamnati na nan tana shirin samar da gyare-gyaren da za su dace da buƙatun kowa.