Daga BASHIR ISAH
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shahararren ɗan jaridar nan, AbdulAziz AbdulAziz, a matsayin Babban Hadimi na Musamman a ɓangaren jaridu.
Abdulaziz ɗan jarida ne da ya ƙware a binciken ƙwa-ƙwaf wanda kuma ya yi shura a soshiyal midiya.
Kafin naɗin nasa, shi ne Hadimi na Musamman Kan Sha’anin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a a Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Tinubu.
A baya, Abdulaziz ya yi aiki tare da kamfanin Media Trust inda ya riƙe muƙamin Mataimakin Babban Edita.
Haka nan, ya kasance mai gabatar da shiri a Trust TV mallakar Media Trust.
Bugu da ƙari, ɗan jaridar ya taɓa aiki da jaridun Leadership da Blueprint da kuma Premium Times.