Tinubu ya naɗa Baba-Ahmed mai bai wa mataimakinsa shawara

Hakeem Baba-Ahmed, a matsayin mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin siyasa a ofishin Mataimakin Shugaban, Kashim Shettima.

Baba-Ahmed da kansa ya sanar da naɗin nasa a shafinsa X a ranar Litinin.

“Lokaci ne da ya kamata in bayyana wa duniya cewa na amsa kira in yi aiki a matsayin Mai Bada Shawara ns Musamman (kan harkokin siyasa) ga Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettim,” in ji shi

Shi ɗin jigo ne a Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), kuma ɗan uwa ga abokin takarar shugabancin ƙasa na Jam’iyyar Labour a babban zaɓen da ya gabata, wato Datti Baba-Ahmed.

Ya ce yanzu ba lokacin zama ana suka ba ne, don haka ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su taya shi da ma ƙasa baki ɗaya addu’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *