Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Mista Shamseldeen Babatunde Ogunjimi a matsayin muƙaddashin Akanta Janar na Tarayya (AGF). Wannan sanarwa ta fito daga mai ba Shugaban Ƙasa shawara Bayo Onanuga, ranar Talata. Naɗin ya fara aiki nan take bayan hutun ritaya da Akanta Janar na yanzu Dakta Oluwatoyin Sakirat Madein ta fara.
Shugaban Ƙasa ya bayyana cewa naɗin Ogunjimi zai tabbatar da sauyin shugabanci cikin sauƙi a fannin kula da baitulmalin ƙasa tare da ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da gwamnatin ta ke yi a harkokin baitulmalin ƙasa. Ogunjimi, wanda shi ne babban darakta mafi girma a ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF), yana da gogewa fiye da shekaru 30 a harkokin kula da kuɗi a ɓangarorin gwamnati da masu zaman kansu.
A lokacin aikinsa, Ogunjimi ya riƙe manyan muƙamai kamar Daraktan Kula da Kuɗaɗe a OAGF da Daraktan Kula da Kuɗi da Asusu a na’aikatar harkokin waje.
Haka kuma, yana da ƙwarewa ta musamman a matsayin ƙwararren akanta, mai binciken zamba, ƙwararren dillalin hannayen jari da kuma masanin tsaro da zuba jari.
Yana da digiri na farko a fannin lissafin kuɗi da digiri na biyu a harkokin kuɗi da lissafin kuɗi.
Shugaba Tinubu ya nuna ƙwarin guiwa kan ƙwarewar Ogunjimi, yana cewa: “Ofishin Akanta Janar na Tarayya na da matuƙar muhimmanci wajen gudanar da harkokin baitulmalin ƙasa. Gwanintar Ogunjimi da ƙwarewarsa za su tabbatar da ci gaba da ingantaccen aiki na wannan muhimmin fanni yayin da muke ci gaba da tafiyar da manufofin gyaran tattalin arzikin ƙasa.”
Haka zalika, Shugaban Ƙasa ya yaba wa tsohuwar Akanta Janar, Dr. Madein, kan ƙoƙarinta da sadaukarwar ta wajen bautawa ƙasa. Dakta Madein za ta yi ritaya ne a ranar 7 ga watan Maris, 2025, bayan kaiwa shekarun ritaya da dokar aiki ta tanada.