Tinubu ya naɗa Gbajabiamila Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Ƙasa

*George Akume ya zama Sakataren Gwamnatin Tarayya

Daga BASHIR ISAH

Shuganan Ƙasa Bola Tinubu, ya naɗa Shugaban Majalisar Wakilai mai barin gado, Femi Gbajabiamila, a matsayin sabon Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Ƙasa.

Yayin da ya naɗa tsohon Gwamnan Jihar Binuwai kuma tsohon Ministan Ayyuka na musamman, George Akume, a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Tinubu ya yi naɗe-naɗen ne a ranar Juma’a, inda tsohon Mataimakin Gwamnan Jigawa, Sanata Ibrahim Hadejia, ya samu muƙamin Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa.

Bayanin naɗe-naɗen na ƙunshe ne cikin sanarwa mai ɗauke da sa-hannun Daraktan Yaɗa Labarai na Fadar Shugaban Ƙasa, Abiodun Oladunjoye.

A cewar sanarwar, “Yayin wani taro da ƙungiyar gwamnoni ta Progressives Governors Forum, Shugaban ya ambaci tsohon Gwamnan Jihar Binuwai kuma tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, George Akume a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya.”

Ya zuwa haɗa wannan labari, majiyarmu ta ce Shugaba Tinubu na kan tattaunawa da dukkanin zaɓuɓɓun gwamnonin Jam’iyyar APC a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *