
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa tsohon shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega a matsayin Mai taimaka masa kuma Kodineta kan harkokin Kiwo.
Mai taimaka wa Shugaban kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya wallafa hakan ta kafar X, ranar Juma’a.
Daga shekarar 2010 zuwa 2015 ne Jega ya riƙe muƙamin shugaban INEC.
Haka kuma a watan Yulin 2024 ne Shugaba Tinubu ya samar da sabuwar ma’aikata mai suna Ma’aikatar Ci-gaban Kiwo.
An samar da ita ne musamman don warware matsalolin da suka jima suna faruwa a tsakanin makiyaya da manoma a sassan Nijeriya.