Tinubu ya naɗa Malagi, El-Rufai, Wike muƙamin minista

*An kasa samun matsaya kan ministocin Kano, Zamfara da Kebbi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ƙarshe dai Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunayen mutane 28 da ya zaɓa a matsayin ministoci, domin naɗa su a matsayin mabobin Majalizar Zartarwar Tarayyar Nijeriya.

Bayan an daɗe ana jiran jerin sunayen ne a jiya Alhamis Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya zo zauren majalisar da ƙarfe 12:05 na rana, inda bayan an yi addu’ar buɗe zaman zauren sai kuma ya bayyana cewa, majalisar za ta shiga wani zama na musamman.

Bayan zaman ne ya fito ya bayyana jerin sunayen mutanen sa Shugaba Tinubu ke so su jagoranci ma’aikatun Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin gwamnatinsa.

Cikin jerin sunayen, akwai mawallafin jaridun Blueprint da Manhaja, Mohammed Idris Malagi, da wasu tsofaffin gwamnoni da suka haɗa da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai da na Jihar Ribas Nyson Wike da kuma na Jihar Jigawa Mohammad Badaru Abubakar, tare da wasu sanatoci da dai sauran manyan ’yan siyasa.

Akpabio ya tabbatar wa kowa da kowa cewa, jerin ba su ƙare ba, saboda har yanzu akwai sauran jihohin da za a gabatar da sunayen ministocinsi a Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ciki har da Kano, Zamfara da Kebbi daga yankin Arewa maso Yamma.

Wata majiya ta shaida wa Blueprint Manhaja cewa, an kasa samun matsaya ne kan waɗanda za su wakilci waɗannan jihohi sakamakon yadda ake samun turjiyar siyasa game da sunayen da Shugaba Tinubu ke son naɗawa a muƙamin.

Majiyar ta ce, an zare sunan tsohon Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje daga ciki ne sakamakon muƙamin Shugaban Jam’iyya na Ƙasa na APC da ake kyautata zaton zai hau, inda Shugaban Ƙasar ya nemi maye gurbinsa da na tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, wanda babban ɗan adawa ne na Ganduje.

Bayanan sun ce, hakan ya janyo mummunar turjiya daga magoya bayan APC a jihar ta Kano, waɗanda suke ganin kamata ya yi a ƙalla a naɗa ɗan takarar gwamnan na jam’iyyar a zaɓen da ya gabata na 2023, wato Nasiru Yusuf Gawuna.

Sai dai kuma, wata majiyar ta shaida wa Blueprint Manhaja cewa, akwai yiwuwar Tinubu zai bai wa Jihar Kano muqamin kujerar minista guda biyu, wanda wannan mataki zai iya rage wata taƙaddamar.

Bugu da ƙari, game da Jihar Zamfara kuma majiyar ta shaida cewa, an samu gaggausar adawa ne busa yunƙurin da ake ganin Fadar Shugaban Ƙasa na yi na naɗa tsohon gwamnan jihar, Muhammad Bello Matawalle, wanda ake kallo a matsayin ya gaza kai bantensa ta kowacce fuska a siyasar jihar da ma cigabanta.

Ita Jihar Kebbi na fama da makamanciyar matsalar, inda mutane da dama ke ganin, kamar tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, shi ma tsohon Gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ana kallon sa a matsayin wanda bai tavuka abin arzikin da ya cancanci zama ministan da zai wakilci jihar ba.

Kan wannan batu dai an zura idanu ga Shugaba Tinubu wajen ganin yadda zai warware wannan zare da abawa.

Cikakken jerin sunayen ministocin da shugaba Bola Tinubu ya aika wa Majalisar Dattawa su ne kamar haka; Abubakar Momoh, Yusuf Maitama Tuggar, Ahmad Dangiwa, Hannatu Musawa, Uche Nnaji, Betta Edu, Dr. Diris Anite Uzoka, David Umahi, Ezenwo Nyesom Wike, Muhammed Badaru Abubakar, Nasir El Rufai, Ekerikpe Ekpo, Nkiru Onyejiocha, Olubunmi Ojo, Stella Okotete, Uju Kennedy Ohaneye, Bello Muhammad Goronyo, Dele Alake, Lateef Fagbemi, Mohammad Idris, Olawale Edun, Waheed Adebanwp, Iman Suleman Ibrahim, Farfesa Ali Pate, Farfesa Joseph Usev, Abubakar Kyari, John Enoh tare da kuma Sani Abubakar Danladi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *