Tinubu ya naɗa Manjo Janar Olufemi a matsayin muƙaddashin hafsan sojojin Nijeriya

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Manjo Janar Olufemi Olatubosun Oluyede a matsayin muƙaddashin Hafsan Sojan Ƙasa (COAS). Wannan naɗi ya fito ne a wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara , Bayo Onanuga, ya fitar ranar Laraba.

Onanuga ya bayyana cewa Oluyede zai riƙe wannan muƙamin na COAS har zuwa dawowar Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, wanda ke fama da rashin lafiya kuma yana karɓar magani a ƙasashen waje.

Manjo Janar Oluyede, mai shekaru 56, shi da Lagbaja abokan karatu aji na 39 a makarantar horar da sojoji. An yi masa naɗin Laftanar a shekarar 1992, inda ya kai matsayin Manjo Janar a watan Satumbar 2020.

Oluyede ya riƙe muƙamai da dama tun bayan naɗinsa a matsayin sojan Najeriya. Ya kasance Platoon kwamanda da adjutant a bataliya ta 65, kuma ya kasance kwamanda a bataliya ta 177 , sannan hafsan soji a Guards Brigade, da kuma Kwamandan makarantar horas da sojoji (Amphibious Training School). Yana da aure kuma shi da matarsa suna da ‘ya’ya uku.