Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da a naɗa Dr. Jamila Bio Ibrahim Ministar Matasa gabanin Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin.
A cewar mai magana da yawun Shugaban Ƙasa a ranar Lahadi, Ajuri Ngelale, Tninubu ya kuma amince da naɗin Mista Ayodele Olawande a matsayin Ƙaramin Ministan Matasa kafin Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin nasa nan gaba.
“Dr. Jamila likita ce wadda ta yi shugabancin Ƙungiyar Cigaban Mata Matasa (PYWF) ba da daɗewa ba.
“Kazalika, ta riƙe muƙamin Hadimar Gwamnan Jihar Kwara kan Muradan Samar da Cigaba Mai Ɗorewa (SDGs).
“Shi kuwa Mista Ayodele Olawande, masanin cigaban al’umma ne kuma shugaban matasa a Jam’iyyar APC.
“Aiki na baya-baya da ya yi shi ne a Ofishin Mai Bada Shawara na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan ƙirƙire-ƙirƙire daga 2019 zuwa 2023,” in ji Ngelale.
Ya ƙara da cewa, Shugaba Tinubu ya buƙaci su biyun da su yi amfani da ƙwarewarsu wajen inganta rayuwar matasa da tabbatar da matasa sun bada gudunmawarsu ga cigaban ƙasa yadda ya kamata.