Tinubu ya naɗa Nkwocha, Kakanda da wasu a muƙamai a Fadar Shugaban Ƙasa

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya naɗa tsohon Editan Jaridar Leadership, Kingsley Stanley Nkwocha, a matsayin Babban Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Yaɗa Labarai a Fadar Shugaban Ƙasa.

An naɗa Nkwocha tare da wasu ne inda za su yi aiki tare a ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa.

Kazalika, Tinubu ya naɗs Tope Fasua a matsayin Mai Bada Shawara na Musamman Kan Harkokin Tattalin Arzikin Ƙasa a ofishin Mataimakin na Shugaban Ƙasa.

Sauran waɗanda aka naɗa masu bada shawara a ɓangarori daban-daban sun haɗa da Sadiq S Jambo da Dr. Muhammad Bulama da Mahmud Muhammad da kuma Ahmed Ningi.

Sanarwar naɗin ta kuma nuna marubuci kuma mai fashin baƙi kan lamurran yau da kullum, Gimba Kakanda, shi ma ya samu shiga inda aka naɗa shi a matsayin Babban Mai Bai wa Matakin Shugaban Ƙasa Shawara kan harkokin bincike da fashin baƙi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *