Daga BASHIR ISAH
A ranar Litinin Shugaban Ƙasa sauke duka jami’an da ke jan ragamar fannin tsaron Nijeriya nan take.
Kazalika, ba tare da ɓata lokaci ba Tinubun ya amince da naɗin waɗanda za su maye gurbin saukakkun.
Waɗanda sabbin naɗe-naɗen ya shafa sun haɗa da:
1 Malam Nuhu Ribadu, Mai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro
2 Manjo Janar C.G Musa, Babban Hafsan Tsaro
3 Manjo T. A Lagbaja, Babban Hafsan Sojoji
4 Rear Admirral E. A Ogalla, Babban Hafsan Sojojin Ruwa
5 AVM H.B Abubakar, Babban Hafsan Mayaƙan Sama
6 DIG Kayode Egbetokun, Muƙaddashin Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda
7 Manjo Janar EPA Undiandeye, Babban Hafsan Tsaron Sirri.
Bugu da ƙari, Shugaban ya amince da naɗin waɗannan jami’ai:
1 Col. Adebisi Onasanya Brigade of Guards Commander
2 Lt. Col. Moshood Abiodun Yusuf 7 Guards Battalion, Asokoro, Abuja
3 Lt. Col. Auwalu Baba Inuwa 177, Guards Battalion, Keffi, Jihar Nasarawa.
4 Lt. Col. Mohammed J. Abdulkarim 102 Guards Battalion, Suleja, Jihar Neja.
5 Lt. Col. Olumide A. Akingbesote 176 Guards Battalion, Gwagwalada, Abuja
Sai kuma jami’an Fadar Shugaban Ƙasa da naɗin ya shafa:
1 Manjo Isa Farouk Audu (N/14695) Commanding Officer State House Artillery
2 Capt. Kazeem Olalekan Sunmonu (N/16183) Second-in-Command, State House Artillery
3 Maj. Kamaru Koyejo Hamzat (N/14656) Commanding Officer, State House Military Intelligence
4 Maj. TS Adeola (N/12860) Commanding Officer, State House Armament
5 Lt. A. Aminu (N/18578) Second-in- Command, State House Armament
Shugaban ya kuma amince da naɗin ƙarin Masu Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman guda biyu da Manyan Hadimai guda biyu:
1 Hadiza Bala Usman Special Adviser, Policy Coordination
2 Hannatu Musa Musawa Special Adviser, Culture and Entertainment Economy
3 Sen. Abdullahi Abubakar Gumel Senior Special Assistant , National Assembly Matters (Senate)
4 Hon. (Barr) Olarewaju Kunle Ibrahim Senior Special Assistant, National Assembly Matters (House of Representatives)
A ƙarshe, Tinubu ya amince da naɗin Adeniyi Bashir Adewale a matsayin Muƙaddashin Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam.
Sanarwar da ke ɗauke da wannan bayanin ta ce, jami’an da ke riƙon ƙwarya za su ci gaba da riƙe muƙamansu ne ya zuwa lokacin da za a tabbatar da su.