Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Alhamis ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ƙasar Chana da ta ƙara Dala biliyan 2 na musayar kuɗi tsakaninta da Nijeriya don faɗaɗa harkokin kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.
Ya kuma yi kira da a sabonta nazari game da Dala biliyan 50 na taimako da ƙasar ta ware wa Afirka wanda Shugaba Xi Jinping ya sanar a shekarar da ta gabata.
A kwanan nan ne Chana da Nijeriya suka sabonta yarjejeniyar musayar kuɗi a tsakanin su wanda ya kai kimanin Yuan biliyan 15 (Dala biliyan 2) don bunƙasa kasuwanci da zuba hannun-jari.
A lokacin da ya karɓi baƙoncin Ministan Harkokin Waje na ƙasar, Wang Yi a Fadar shugaban ƙasa dake Abuja, Shugaba Tinubu ya ce hakan zai taimaka wa samar da ayyukan ci-gaba a Nijeriya tare da ƙara ƙarfafa alaƙa a harkoki daban-daban tsakanin ƙasashen.
Tinubu ya kuma nemi Chana ta taimaka wa Nijeriya a ƙoƙarinta na neman kujera a Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya.
Kazalika, ya yi godiya ga Shugaban Chana bisa tarba ta karamci da ya yi masa a lokacin da ya ziyarci ƙasar a shekarar 2024.
Har’ilayau, Shugaba Tinubu ya ce a shirye Afirka ta ke musamman Nijeriya ta samu ci-gaban don ta kasance mai gogayya da suaran ƙasashe a sassan duniya ta hanyar maraba da taimako a ayyukanta na ci-gaba.
A nasa jawabin, Ministan ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa ƙoƙarinsa na hangen nesansa a jagorancin ya ke yi wa Nijeriya da jajircewa wajen neman gina Afirka da al’ummarta.