Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya sa hannu a kan umarnin shugaba guda huɗu, da nufin rage wasu nau’o’in haraje-haraje ga al’ummar ƙasar.
Ɗaya daga cikin umarnin shugaban ƙasar shi ne dakatar da harajin kashi biyar a kan ayyukan wayoyin sadarwa da kuma dakatar da harajin da aka tsawwala a kan kayan da ake sarrafawa a cikin gida.
Mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan ayyuka na musamman da al’amuran sadarwa, Dele Alake ya faɗa ranar Alhamis cewa shugaban ƙasar ya kuma sa hannu a kan Dokar Kuɗi ta 2023, wadda a yanzu ta jingine fara aiki da sauye-sauyen da ke cikin dokar daga ranar 23 ga Mayun 2023 zuwa 1 ga Satumban 2023.
A cewar mai magana da yawun shugaban ƙasar, an yi hakan ne domin tabbatar da bin ƙa’idar ba da sanarwa ko notsi na aƙalla kwana 90 ga sauye-sauyen haraji kamar yadda yake ƙunshe a Manufar Tattara Haraji ta Masa ta 2017.
Shugaba Tinubu ya kuma rattaɓa hannu a kan dokar karɓar harajin shigo da kaya da aka yi wa garambawul ta 2023, inda ya canza ranar fara aiki da dokar harajin daga 27 ga watan Maris zuwa 1 ga Agustan 2023 kamar yadda yake cikin Manufar Karɓar Haraji ta Ƙasa.
Tinubu ya kuma bayar da umarnin dakatar da wani sabon haraji mai suna Green Tax da aka ɓullo da shi kan robobin da ake amfani da su sau ɗaya, sannan a jefar, ciki har da mazuban roba da goran roba, ya kuma dakatar da wani nau’in haraji da ake karɓa a kan wasu nau’o’in motoci da ake shiga da su ƙasar.