Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rattava hannu kan ƙudirin dokar da ke neman tsawaita wa’adin ritayar alkalan babbar kotun ƙasar daga shekaru 65 zuwa 70.
Shugaban Ƙasa ya amince da ƙudirin dokar shekarun ritayar alƙalan Babbar Kotun ƙasar rana Alhamis, 8 ga Yuni, 2023.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Abiodun Oladunjoye, Daraktan Yaɗa Labarai na Shugaban Ƙasa, ya ce Tinubu ya sanya hannu kan dokar “Constitution of the Federal Republic of Nigeria, 1999 (Fifth Change) (No. 37), 2023,” wanda Majalisar Ƙasa ta 9 mai barin gado ta gabatar da shi.
Tare da sanya hannu kan dokar gyaran kundin tsarin mulki, shekarun ritayar jami’an shari’a da haƙƙin fansho sun kasance an daidaita, tare da sauran batutuwa masu alaƙa.
A yayin da yake rattaɓa hannu a kan ƙudirin gyaran fuska ga dokar, Tinubu ya yi alƙawarin jajircewar gwamnatinsa wajen ƙarfafa ɓangaren shari’a, tabbatar da bin doka da oda, da bai wa jami’an shari’a damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Amincewar da shugaban qasa ya yi wa ƙudirin gyara na nufin shekarun ritaya na alƙalan babbar kotuna ya sauya daga shekaru 65 zuwa 70.