Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Abu Dhabi na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) domin halartar tarurrukan da za a yi na Satin batutuwan Ci-gaba na Abu Dhabi (ADSW).
Shugaban ƙasar UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan musamman ya aika wa Shugaba Tinubu saƙon gayyatar sa zuwa taron.
Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai ta kafafen sadarwa, Dada Olusegun ya bayyana hakan a kafar X inda ya ɗora wani faifan bidiyo da ke nuna yadda Tinubu ya isa ƙasar.
Ya ce taken taron shi ne ‘The Nexus of Next: Supercharging Sustainable Progress’ wanda za a gudanar daga ranar 12 zuwa 18 da watan Junairu a birnin Abu Dhabi.
Taron zai haɗa jagororin ƙasashen duniya ne don tattauna batutuwan ci-gaba da nasarori a harkokin tattalin arziƙi da ci-gabansa.
Ya kuma ce ana sa ran Shugaba Tinubu zai gabatar da jawabi ne akan gyare-gyaren harkokin Gwamnatinsa musamman akan lamuran ci-gaba a gas, sufuri, lafiya da ci-gaban tattali.
Ya ƙara da cewa, Tinubu da tawagarsa za su tattauna da gwamnatin ƙasar don ƙarfafa alaƙa a ɓangarori daban-daban domin faɗaɗa ayyukan ci-gaba a Nijeriya.
Jami’an da suka raka shugaban ƙasar sune; Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar da Shugaban ma’aikatan Fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila da kuma shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.