Tinubu ya shigar da ƙara don hana LP, PDP dakatar da tattara sakamakon zaɓe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ɗan takararta na Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, sun shigar da ƙara domin hana Jam’iyyar Labour Party (LP) da PDP yin wani abu na hana tattarawa da bayyana sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.

A ƙarar da aka shigar gaban Babbar Kotun Tarayya dake Kano mai lamba FHC/KN/CS/43/2023, an haxa da Action Alliance da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) a matsayin waɗanda ake ƙara, yayin da mataimakin shugaban Jam’iyyar APC, Kashim Shettima a matsayin mai gabatar da ƙara.

Masu gabatar da ƙara a cikin wata takardar sanarwa da aka shigar tare da asalin sammacin, sun buƙaci kotun da ta bada umarnin hana waɗanda ake ƙara dakatar da tattara sakamakon zaɓe da kuma bayyana sakamakon saboda “lalacewar ba za ta biya cikakkiyar diyya ga raunin da za a iya samu a kan masu ƙarar ba idan da waɗanda ake tuhuma suka dakatar da tattara sakamakon.”