Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Nijeriya a ranar Lahadi domin halartar taron ƙoli na haɗin gwiwar ƙasashen Larabawa da Musulunci a Saudiyya. Taron zai gudana ne a Riyadh ranar Litinin, inda zai mayar da hankali kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya. Tinubu zai halarci taron ne bisa gayyatar Sarki Salman da Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Asabar, inda ya ce, “Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga Abuja a ranar Lahadi zuwa Riyadh, Saudiyya, domin halartar taron ƙoli na haɗin gwiwa na ƙasashen Larabawa da Musulunci, wanda zai maida hankali kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya.”
Taron zai fara a ranar Litinin, 11 ga watan Nuwamba, 2024, a Riyadh, Saudiyya, wanda aka shirya shi ne bisa gayyatar Sarki Salman da Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman. Wannan taro na bana na biyo bayan wanda aka gudanar a shekara ta bara a cikin wannan birni na Saudiyya.
A yayin taron, ana sa ran Shugaba Tinubu zai yi magana kan rikicin Isra’ila da Falasɗinu, inda zai jaddada kira mai ƙarfi daga Nijeriya na a samu tsagaita wuta nan take da kuma buƙatar samun mafita cikin lumana. Shugaban ƙasa zai nuna damuwar Nijeriya game da rikicin tare da yin kira a hanzarta samar da maslaha ta dindindin.
Bugu da ƙari, Nijeriya za ta yi ƙoƙarin neman sake farfaɗo da tsarin warware rikicin cikin hanyar ƙirƙirar ƙasashe biyu (Isra’ila da Falasɗinu) domin samun zaman lafiya mai ɗorewa a yankin. Shugaban ƙasa ba zai tafi shi kaɗai ba, wasu manyan jami’an gwamnati kamar ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar,mai ba da shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ministan bayani, Mohammed Idris da daraktan hukumar leƙen asiri ta Ƙasa (NIA), Mohammed Mohammed, za su kasance tare da shi a wannan tafiya.