Tinubu ya taya ƴan Nijeriya shida murna bisa samun babbar kyautar kimiyya ta Amurka

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya ƴan Nijeriya shida da Shugaba Joe Biden ya bada sunayensu cikin mutane 400 da za a bai wa kyautar ƙwarewar karatun kimiyya da injiniyanci (PECASE) ta shugaban ƙasa a Amurka.

A shekarar 1996 ne aka ƙirƙiri babbar kyautar a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bill Clinton, wadda ita ce kyautar lambar yabo mafi girma da gwamnatin Amurka ke bai wa ƙwararrun ɗaliban kimiyya da injiniyanci masu tasowa.

Hukumomin Amurka 14 da suka shiga cikin shirin na wannan shekarar su ne suka ɗauki nauyin waɗanda aka bai wa kyautukan a ranar 14 ga watan Junairu.

A wata sanarwa da Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Alhamis, Shugaba Tinubu ya jinjina wa ƴan Nijeriyar da suka samu nasarori a ɓangarorin kimiyya da fasaha da harkar injiniyanci.

Ya ce hakan wani fage ne da ke nuna fintinkau da ƴaƴan Nijeriya suka yi a cikin gida da kuma mataki da duniya.

Ya kuma nemi su yi amfani da ƙwarewarsu wajen bada gudunmawa ga ci-gaban Nijeriya a ƙarƙashin shirinsa na sabonta ƙasar.

Waɗanda aka karrama daga Nijeriya sun haɗa da Azeez Butali da Farfesa Ijeoma Opara da Oluwatomi Akindele da Eno Ebong da Oluwasanmi Koyejo da kuma Abidemi Ajiboye.