Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya Shugaba Donald Trump murna bayan sake zaɓan sa da aka yi karo na biyu a matsayin shugaban ƙasar Amurka na 47.
Shugaba Tinubu ya ce ya na ƙoƙarin ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin Nijeriya da Amurka duk da ƙalubalen damanmaki da duniyar yau ke ciki, ya na mai cewa haɗin kai a harkar tattali, inganta zaman lafiya da matsalolin da ke addabar al’ummar ƙasashen biyu su ake neman a samarwa mafita.
Ya ce, nasarar da Trump ya samu ta nuna yadda al’ummar ƙasar suka yarda da shugabancinsa inda ya taya su murna ga ƙoƙarinsu na tabbatar da ɗorewar demokraɗiyya.
Ya kuma ce dawowarsa karagar mulkin za ta taimaka wajen inganta tattali da ci-gaban alaƙar da ke tsakanin Nahiyar Afirka da Amurka, ya na mai fatan hakan ya zama sababi na samun zaman lafiya da nasarori ga al’umma.