Tinubu ya umarci a karɓe Jami’ar Nok dake Kaduna da mayar da ita ta Tarayya

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci Gwamnatin Tarayya da ta karɓe iko a Jami’ar Nok dake Kachia a Jihar Kaduna da mayar da ita ta Tarayya.

Haka na zuwa ne bayan da Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta bada umarni a karo na ƙarshe da a karɓe Jami’ar, wadda mai zaman kanta ne zuwa ta Gwamnatin Tarayya.

A yanzu haka dai an mayar da sunanta ‘Federal University of Applied Sciences, Kachia’, wanda hakan wani ɓangare ne na cika alƙawarin da aka yi wa al’ummar kudancin jihar.

A lokacin da ya ke magana a taron miƙa mallakar makarantar da EFCC ta yi ga Gwamnatin Tarayya a Fadar shugaban ƙasa, Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya bayyana hakan a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin inganta ƙasa da gwamnatinsu take yi.

Ya ce wannan nasara ce ga ƙasar da kuma Jihar Kaduna, wanda shi ne abu na farko acikin jaddawalin ayyukan Majalisar Zartarwar, ya na mai cewa akwai buƙatar a yaba wa Shugaba Tinubu akan al’amarin.

A wata sanarwa da babban mai taimaka wa Shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha ya fitar, Shettima ya tabbatar cewa nan take jami’ar za ta fara aiki.

“Shugaban ya umarci Ministan Ilimi da ya tabbatar da sanya jami’ar a kasafin 2025, ta yadda zuwa Satumba za ta yi ɗibar farko ta ɗalibai”, inji Shettima.

Haka kuma ya ce gwamnati za ta cigaba da ƙoƙarin bunƙasa ayyuka ci-gaban a Kudancin Kaduna musamman kan batun da ya shafi gina titina.

A nasa jawabin, Gwamna Uba Sani na jihar, ya yi godiya ga Shugaba Tinubu bisa samar da jami’ar kimiyya a kudancin jihar, ya na mai bayyana hakan a matsayin babbar nasara ga al’ummar yankin da ma ƴan Nijeriya baki ɗaya.