Shugaba Tinubu ya umarci ministan shari’a kuma lauyan gwamnati, Lateef Fagbemi da ya sake duba tuhume-tuhume na cin amanar ƙasa da aka shigar kan wasu ƙananan yara da kuma rashin basu abinci mai gina jiki a gaban babbar kotu da ke Abuja.
Wannan lamarin ya janyo cece-kuce a ƙasa da ma duniya ba ki ɗaya kan yadda ƙasar ke gudanar da sha’anin ƴancin yara. Da wannan ne shugaban ƙasa ya umarci lauyan gwamnati ya duba lamarin domin bayar da sabbin shawarwari kan yadda za a shawo lamarin.
Mutane da dama na ta Allah wadai kan wannan lamarin domin ya nuna irin yadda gwamnatin ke kula da haƙƙin ƙananan yara.
A zaman kotun da akayi, Mai Sharia Obiora, ya bada belin yaran su kusan 70 kan wasu sharuɗa masu tsaurin gaske. Abinda ya ɗauki hankalin mutane shine yadda a na tsakiyar shari’a wasu daga cikin yaran suka faɗi a sume saboda tsananin yunwa. Kowanne an bada belin shi a kan kuɗi Naira miliyan 10.
Sai dai ƙungiyoyin fararen hula da dama sun yi Allah wadai da wannan lamarin inda suka buƙaci gwamnati tai gaggawar sakin waɗannan yaran.