Tinubu ya yaba wa gwamnoni bisa goyon bayan ƙudirin kwaskwarimar haraji

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana jin daɗinsa ga ƙungiyar gwamnonin Nijeriya bisa goyon bayan ƙudirin kwaskwarimar haraji guda huɗu da ya miƙa wa majalisa domin tantancewa.

Ya kuma jinjina wa gwamnonin kan namijin ƙoƙarin da suke yi wajen jagorancin al’ummarsu da samar da haɗin kai tsakanin jagororin ƙasar ba tare da la’akari da yare, yanki ko kuma banbancin siyasa ba wanda hakan wani mataki ne da zai haɓaka ci-gaba a Nijeriya.

A wata takarda da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Alhamis, Tinubu ya yaba wa Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman AbdulRazaq sakamakon cimma matsaya da sauran mambobinsa game ƙudirin.

Haka kuma Shugaba Tinubu ya yaba wa ƙungiyoyin ‘Progressive Governors Forum’ da ‘Northern Governors Forum’ da sauran ƙungiyoyin da suka cire banbancin siyasa wajen cimma matsaya guda ɗaya akan batun.

Sanarwar ta ƙara da cewa, Tinubu ya bayyana manufofin gyaran harajin kamar haka; don amfanin al’umma, samar da ci-gaban ƙasa, gogayyar tattalin arziƙin Nijeriya da na wasu ƙasashe da kuma janyo ra’ayoyin masu zuba jari a ciki da wajen Nijeriya, ya na mai cewa hakan abu ne mai muhimmanci.

Kazalika, Tinubu ya bayyana gwamnonin a matsayin abokanan da ke bada gudunmawa wajen gina ƙasa, ya na mai cewa zai cigaba da aiki tare da su ga ayyukan inganta ƙasa.

Ya kuma yi kira ga masu-ruwa-da-tsaki da bada gudunmawarsu yayin da majalisa take cigaba da ƙoƙarin kammala aikin tantance ƙudirin.