Tinubu ya yi murna da ceto ɗaliban Kuriga

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi farin ciki da ceto wasu ɗaliban Kuriga a Jihar Kasuna da jami’an tsaro suka yi, tare bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewar gwamnatinsa za ta tabbatar da tsaro a makarantu.

Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da ya mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

“Shugaban Ƙasa ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin gwamnatinsa na amfani da ingantattun dabaru wajen ganin an samu tsaro mai inganci a makarantunmu,” in ji sanarwar.

Kimanin ɗalibai 287 ne ‘yan bindiga suna yi awon gaba da su a farkon watan Maris a yankin Kuriga cikin Ƙaramar Hukumar Kuriga a Jihar Kaduna.

A Talatar da ta gabata ‘yan bindigar suka buƙaci a biya kuɗin fansa Naira biliyan ɗaya kafin su sako ɗaliban.