Daga MAHDI M. MUHAMMAD
A Juma’ar da ta gabata Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da wasu sababbin naɗe-naɗe da ya yi a wasu muhimman hukumomin Gwamnatin Tarayya, domin su jagorance su.
An naɗa sabon shugaban hukumar tara haraji (FIRS):
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya amince da naɗin Honarabul Zacch Adedeji a matsayin sabon shugaban riqo na Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Tarayyar Nijeriya (FIRS) da gaggawa.
Shugaban ƙasar ya umarci tsohon shugaban FIRS, Muhammad Nami, da ya ci gaba da hutun watanni uku kafin ya yi ritaya kamar yadda dokar ma’aikatan gwamnati (PSR) 120243 ta tanada nan take.
Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a Abuja, ya ce Hon. Zacch Adedeji zai yi aiki na tsawon kwanaki 90 kafin a tabbatar da shi a matsayin babban Shugaban Hukumar Tara Harajin Cikin Gida ta Tarayya na tsawon shekaru huɗu a matakin farko.
Hon. Zacch Adedeji ya yi digiri na farko a fannin lissafin kuɗi daga Jami’ar Obafemi Awolowo.
A baya-bayan nan ya yi wa ƙasa hidima a matsayin mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin kuɗaɗen shiga, bayan da ya yi wa ƙasa hidima a matsayin kwamishinan kuɗi na Jihar Oyo.
An naɗa majagabar hukumar shirya zuba jari ta Nijeriya:
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Misis Delu Bulus Yakubu a matsayin majagabar Hukumar shirya Zuba Hannun Jari ta Nijeriya (NSIPA), har sai Majalisar Dattawa ta tabbatar da ita.
Hukumar Shirye-shiryen Zuba Jari ta Ƙasa (NSIPA), an sanya hannu kan sabuwar dokarta a ranar 22 ga Mayu, 2023.
Delu Bulus Yakubu ta samu digirin digirgir a fannin aikin gona daga Jami’ar Jiha ta Fasahar Bio-Technology da ke Kharkiv na ƙasar Ukraine, wadda ta shafe sama da shekaru 15 tana da gogewa wajen gudanar da shirin zuba jari na zamantakewa.
Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Cif Ajuri Ngelale, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ya ce shugaban ƙasar na sa ran sabuwar wadda aka naɗa ɗin za ta samar da cigaba mai ɗorewa a NSIPA, a daidai lokacin da ya ƙuduri aniyarsa aiwatar da ajandar sabunta gwamnatinsa.
An naɗa shugaban hukumar kula da ’yan gudun hijira da baƙin haure:
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naxin Mista Aliyu Tijani Ahmed a matsayin sabon shugaban Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira da Bakin Haure (NCFRMI).
Malam Aliyu Tijani Ahmed wanda ya samu digirin farko da na biyu a fannin zamantakewar al’umma kuma ya tava riƙe muƙami a gwamnatin jihar Nasarawa a matsayin sakataren gwamnatin jihar (SSG), kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu da kuma kwamishinan ilimi.
Mai ba wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Cif Ajuri Ngelale, ya ce, naɗin ya fara aiki nan take.