Tinubu ya yi wa Atiku ƙafar baya a Zamfara

Daga AMINU AMANAWA

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa babban abokin karawarsa Atiku Abubakar ƙafar baya a zaɓen shugaban ƙasa na jihar Zamfara.

Baturen zaɓen jihar Zamfara Farfesa Kasim Shehu ya sanar da cewa Bola Tinibu na jam’iyyar APC ya samu ƙuri’u dubu 298, 396 yayin da Atikun ke biye masa da ƙuri’u dubu 193, 978.

Tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP ya samu ƙuri’u 4044 yayin da Peter Obi na Labour ke da yawan ƙuri’u dubu 1,660.

Yayin sanarwar dai baturen ya ce hukumar ta soke zaɓen runfuna saboda rikice-rikice da wasu “Yan matsalolin da ba’a rasa ba 167.