Daga USMAN KAROFI
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa muƙaddashin hafsan sojojin Nijeriya Olufemi Oluyede ƙarin girma daga manjo janar zuwa laftanar janar.
Bikin ƙarin girman ya faru ne fadar shugaban ƙasa tare da halartar wasu manyan sojoji da su kai rakiya tare da babban ministan tsaro.
Idan ba mu mance ba, shugaban ƙasa ya naɗa Olufemi a mastayin muƙaddashin hafsan sojoji bayan hutun rashin lafiya da Taoreed Lagbaja ya ɗauka.