Tinubu ya yi watsi da rahoton Tarayyar Turai kan zaɓen 2023

Daga BASHIR ISAH

Fadar Shugaban Ƙasar Nijeriya ta yi watsi da rahoton da Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) ta fitar kan babban zaɓen 2023 da ya bai wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na Jam’iyyar APC damar zama Shugaban Nijeriya.

Cikin Sanarwar da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Sahwara Kan Ayyuka na Musamman, Sadarwa da Tsare-tsare, Mr Dele Alake, ya fitar a ranar Lahadi, Fadar ta ce babu gamsassun hujjoji da ƙungiyar ko danginta suka bayar da za su iya ƙalubalantar sahihancin sakamakon babban zaɓen na 2023.

A cewar Alake, rahoton Ƙungiyar Tarayyar Turan rahoto ne mara inganci wanda aka shirya shi ta hanyar taƙaitawa a kan rumfunan zaɓe ƙasa da 1000 daga cikin 176,000 da aka yi amfani da su yayin zaɓen.

Ya ce, “Wani lokaci a watan Mayun da ya gabata, mun kwarmata wa ƙasa ta hanyar sanarwar mane labarai kan cewa akwai wata cibiya da ke shirin ɓata sahihancin babban zaɓen da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta gudanar a 2023.

Ya ƙara da cewa, abin harin cibiyar shi ne zaɓen shugaban ƙasa wanda ɗan takarar Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya lashe zaɓen cikin aminci.

Ya ce, “tun da yanzu cibiyar ta miƙa rahotonta na ƙarshe a kan zaɓen, a yanzu muna iya sanar da ‘yan Njeriya da ma duniya baki ɗaya cewa ba mu da masaniya kan makirce-makircen da Tarayyar Turai ke yi na ci gaba da nuna son kai da iƙirarin da aka yi kan sakamakon zaɓe.

“Muna jaddada cewar zaɓukan 2023, musamman na shugaban ƙasa wanda Shugaba Bola Tinubu na APC ya lashe, sahihi ne, an yi adalci, ya kuma gudana cikin zaman lafiya, shi ne kuma babban zaɓe mafi tsafta da aka shirya a Nijeriya tun 1999,” in ji Alake.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *