Tinubu ya zama shugaban ƙasa na farko da ya naɗa mataimakin Darakta Janar a DSS

Daga USMAN KAROFI

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗa Folashade Arinola Adekaiyaoja fsi+, fdc, a matsayin mataimakiyar Darakta Janar na hukumar tsaro ta DSS.

Naɗin, wanda shine na farko da wani shugaban ƙasa ya yi, ya samu yabo daga ma’aikatan DSS na yanzu da wanda suka yi ritaya, waɗanda suka ce wannan mataki zai dawo da ƙwarewa a hukumar.

Shugaba Tinubu ya yi wannan naɗin ne bayan shawarar darakta janar na DSS ta hannun mai ba da shawara kan tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, don inganta tsarin aikin hukumar bisa ƙa’idojin da aka kafa tun farko.

Adekaiyaoja, ‘yar asalin Jihar Kogi, ta samu goyon baya daga jami’ai masu yawa da suka bayyana ta a matsayin mai cancanta sosai. Ana ganin wannan naɗi a matsayin wani ɓangare na sauye-sauyen da sabon darakta janar, Oluwatosin Ajayi, ya yi alƙawarin aiwatarwa don inganta hukumar tsaron DSS zuwa matakin duniya.