Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta gargaɗi jam’iyyun adawa a ƙasar da kada su yi farin ciki da wuce gona da iri game da kayen Kamala Harris, mataimakiyar shugaban ƙasa a Amurka a zaɓen shugaban ƙasa, inda ta ce Shugaba Bola Tinubu zai sake lashe zaɓen a shekarar 2027.
An sanar da tsohon shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump a matsayin wanda ya lashe zaɓen a ranar Laraba, inda ya kayar da Harris cikin wata babbar nasara da ta jawo ce-ce-ku-ce a duniya baki ɗaya. Trump mai shekaru 78 ya zama shugaban ƙasa na 47 kuma tsofaffin wanda ya taba lashe zaɓen shugaban ƙasa a tarihin Amurka.
Ɗan takarar jam’iyyar Labour Party, Obiora Ifoh, ya bayyana zaɓen Amurka wanda aka sa ido a kai a duniya gaba daya, a matsayin gwajin gaskiya na dimukraɗiya. Ya ce hukumar INEC na da abubuwa masu yawa da za ta koyi daga zaɓen da aka kammala, musamman ganin yadda al’ummar Amurka suka yi watsi da tasirin gwamnati mai ci, wanda har yanzu ya na da muhimmanci a nahiyar Afirka, musamman a tsarin zaɓen Nijeriya.
Shi ma da yake mayar da martani, mai magana da yawun New Nigeria Peoples Party, Ladipo Johnson, ya bayyana cewa duk da cewa tsarin zaɓen Amurka na da wahala kuma ya ci gaba sosai, yana mamakin lokacin da Nijeriya za ta kawo ƙarshen lamari irin na shugabanni masu ƙarfi da ke amfani da matsayi da kuma amfani da hukumar tsaro don tsoratar da ‘yan adawa.
Sai dai babban daraktan yaɗa labarai na jam’iyyar APC, Bala Ibrahim, ya gargaɗi ‘yan adawar da kada su yi sakaci da sakamakon zaɓen Amurka, inda ya ce tsarin zaɓe na ƙasashen biyu ya bambanta. Bala, wanda ya yi magana da wakilinmu a wata hira, ya bayyana cewa tasirin gwamnati mai ci ba ya aiki idan al’umma suka haɗu da murya ɗaya, kamar yadda aka gani a nasarar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari a kan Shugaba Goodluck Jonathan a shekarar 2015.
Kakakin jam’iyyar APC ya bayyana tabbacin cewa nan ba da daɗewa ba, idan ‘yan Nijeriya suka fara girbar romon sauye-sauyen tattalin arzikin da Shugaba Tinubu ya kafa, za su yaba masa kuma su nemi ya ci gaba da mulki. Ya ce jam’iyyar ba ta jin tsoron barazanar ‘yan adawa, sai dai ya gargaɗi cewa ba za a bari harkokin kasar su faɗa hannun ‘yan adawa ba, waɗanda yawancinsu har yanzu suna fama da rikicin shugabanci.