Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Shugaban Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC), Nasir Isa Kwarra, ya bayyana cewa, Shugaba Bola Tinubu zai bayyana sabbin ranakun da Nijeriya za ta gudanar da ƙidayar jama’a da kuma gidaje.
Shugaban NPC ya shaidawa manema labarai a ranar Alhamis bayan ganawarsa da shugaban ƙasar cewa ci gaba da gudanar da ƙidayar jama’a zai haifar da ƙarin kuɗaɗe.
Kidayar da gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta tsara tun daga ranar 3 zuwa 7 ga watan Mayun 2023 an ɗage shi zuwa ranar da gwamnatin Tinubu ta tantance.
Bayan ganawa da shugaban ƙasar a ranar Alhamis, Kwarra ya ce, ya yi masa bayani kan shirye-shiryen hukumar na ƙidayar jama’a.
Ya ce, shugaban qasar ya yi cikakken bayani kan wasu tsare-tsare na wannan atisayen amma ya bayyana cewa ƙarin jinkirin gudanar da lidayar zai kai wa gwamnati ƙarin farashi.
Sai dai ya bayyana cewa shirye-shiryen atisayen da tuni ya laƙume Naira biliyan 100 babban jari ne ga ƙasar nan, inda ya ƙara da cewa atisayen da za a yi a baya ba za su yi tsada ba.