Tinubu zai yi wa shugabannin duniya jawabi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da jawabi a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 78 a hedkwatar majalisar da ke New York a ranar Talata 19 ga watan Satumba.

Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya na Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa Tinubu, a ziyararsa ta farko zuwa Majalisar, zai yi jawabi ga shugabannin ƙasashen duniya da yammacin wannan rana.

Shugaban na Nijeriya zai kasance shugaban Afrika na biyar da zai yi jawabi a rana ɗaya daga cikin taron, kamar yadda jerin sunayen masu gabatar da ƙara daga ofishin shugaban majalisar suka bayyana.

A cikin jerin sunayen, Tinubu zai kasance mai magana na 14 a cikin shugabannin 20 da aka shirya yin jawabi a ranar farko.

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, mai magana na 10, zai kasance shugaban Afrika na farko da zai yi jawabi a zaman safiya na Majalisar.

A zaman da za a yi na tsakar rana, ana sa ran shugabannin Afirka biyar za su yi jawabi a wurin taron.

Shugaban na Nijeriya zai gabatar da jawabinsa ne da misalin ƙarfe 6 na yamma (11pm agogon Nijeriya) ga shugabannin ƙasashen duniya yayin zaman da za a yi da yammacin ranar.

Shugaban ƙasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ne zai kasance shugaban Afrika na farko da zai yi jawabi a zaman na yammacin ranar, sai kuma shugaban ƙasar Moroko, Aziz Akhannouch da shugaban Mozambique Filipe Nyusi.

Shugaban ƙasar Senegal, Macky Sall, shi ne zai kasance na farko da zai yi jawabi a wajen taron, kuma shugaba na ƙarshe a rana ta farko.

Shugaban ƙasar Brazil, Luiz da Sliva ne zai kasance shugaba na farko a duniya da zai gabatar da jawabinsa ga taro na 78 kamar yadda aka saba, sannan shugaban Amurka, Joe Biden, mai magana na biyu na gargajiya, ya kasance ƙasar mai masaukin baƙi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, za a buɗe taro na 78 na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA 78) a ranar Talata 5 ga Satumba tare da rantsar da sabon Shugaban Ƙasa Dennis Francis, na Trinidad and Tobago, wanda zai ɗauki riga na tsawon watanni 12 masu zuwa.

Za a gudanar da babban muhawarar ne daga ranar 19 ga Satumba zuwa 29 ga Satumba.

Taken babban taron wanda ya haɗa da muhawara baki ɗaya shi ne sake gina amana da kuma sake farfaɗo da haɗin kan duniya,  ƙarfafa ayyukan ajandar 2030 da manufofinta na cigaba mai ɗorewa don samar da zaman lafiya, wadata da cigaba ga kowa.