Tinubu zai yi wa ‘yan ƙasa jawabi a yau

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu zai yi wa ‘yan ƙasa jawabi da misalin ƙarfi 07:00 na dare yau Litinin.

Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da ta fito ta bakin mai bai wa Tinubu shawara kan ayyuka na musamman da harkokin sadarwa, Dele Alake.

Sanarwar ta ce ana buƙatar gidajen talabijin da rediyo da sauransu, da su jona da Tashar Talabijin ta Ƙasa da kuma Tashar Rediyo ta ƙasa don yaɗa jawabin Shugaba Ƙasar kai tsaye.

Sai dai sanarwar ba ta fayyace dalilin da ya sa Tinubun zai yi ‘yan ƙasa jawabin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *