Tiwita za ta ci gaba da aiki a Nijeriya nan ba da daɗewa ba – Lai

Gwamnatin Tarayya ta ce nan ba da daɗewa ba za ta ɗage dokar haramta harkokin  microblogging da Tiwita a Nijeriya.

Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya sanar da hakan jim kaɗan bayan kammala taron mako-mako na Majalisar Zartarwa a Abuja, wanda ya gudana ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo.

Lai ya bayyana hakan ne yayin da yake ƙarin bayani dangane da tattaunawar da ake yi da masu harkar micro-blogging wanda a cewarsa galibinsu sun amince da dokokin da aka gindaya musu.

Ministan ya ƙara da cewa, ɓangarorin da ba a rigada an daddale ba a kansu sun haɗa da batun kamfanin Tiwita ya ya buɗe ofishinsa tare da zuba ma’aikata waɗanda za su kasance wakilan ƙasa.

Game da samar da ofishinsa a  Nijeriya kuwa, Lai ya ce duk da kamfanin na Tiwita ya amince da ƙa’idojin da aka shimfiɗa masa, sai dai kamfanin ya ce ba zai iya samar da ofishin ba sai a 2022.

Ministan ya ce yana da tabbacin komai zai daidaita nan da ‘yan makonni game da Tiwita duba da yadda ‘yan Nijeriya suke ɗaukin ci gaba da amfani da shafin a ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *