Toshe hanyar abinci a matsayin makami

Daga IBRAHIM SHEME

Toshe wa mutane hanyar da abinci zai isa gare su wani makami ne da ake amfani da shi a lokacin yaƙi. An yi amfani da shi a lokacin Yaƙin Basasar Nijeriya, wato Yaƙin Biyafra. Manufar wannan matakin ita ce a karya lagon abokan gaba, a rage masu ƙarfi, kuma a tilasta masu su aje makaman su.

To amma Majalisar Ɗinkin Duniya ta haramta ɗaukar irin wannan matakin a kan farar hula. Duk wanda aka kama ya yi hakan, ya aikata babban laifi; ana iya gurfanar da shi a Kotun Miyagun Ayyuka ta Duniya (ICC). Sashe na  8(2)(b)(xxv) na Dokar ICC ta shekarar 1998 ya tabbatar da hakan. Amma wasu ƙasashen su na karya dokar, irin su Yemen da Siriya inda ake yaqi.

Shin Nijeriya na yaƙi da wata ƙasa ne? Amsar ita ce a’a. Tunda haka ne, ya aka yi a makon jiya Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Dillalan Abinci da Shanu ta Nijeriya (AUFCDN) ta ƙaƙaba wa jihohin kudancin ƙasar nan takunkumin sayar masu da abinci ta hanyar tare motocin ɗaukar abinci da ke zuwa Kudu, a daidai garin Jaba na Jihar Kwara? Shin ƙungiyar ta san da dokar duniya kan irin wannan matakin kuwa?

Ƙungiyar ta ce ta yanke shawarar ne saboda gwamnati ta kasa magance kashe ‘yan Arewa da ake yi a Kudu idan rikicin ƙabilanci ya tashi. Don haka ta hana tireloli masu yawan gaske maƙare da hatsi, kayan miya da shanu su tsallaka Kogin Kwara.

Kafin ƙungiyar ta fara aiwatar da matakin, sai da ta ba gwamnati wa’adin kwana bakwai na ta biya mata wasu buƙatu, ciki har da biyan diyyar naira biliyan ɗaya tare da janye haraji kala-kala da ake tursasa ‘yan kasuwa su biya a hanyar su ta zuwa Kudu, kuma a yi yarjejeniyar cewa daga yanzu idan rikicin ƙabilanci ya tashi, har aka kai wa ‘yan Arewa hari, to za su janye kayan sayarwar su.

Shugaban ƙungiyar, Alhaji Muhammad Tahir, ya faɗa wa ‘yan jarida a Abuja cewa an kashe ‘yan Arewa 151 a lokacin rikicin #EndSARS da aka yi a Oktoba da ya gabata, kuma an kashe mutum 100 a rikicin Sasa, Ibadan, wanda aka yi kwanan nan a Jihar Oyo.

A ranar Laraba ta makon jiya kuma, Sakataren Kuɗi na AUFCDN, Alhaji Kabiru Salisu, ya bayyana cewa sun kafa wani kwamiti da zai toshe hanyar zuwa Kudu a daidai Jihar Neja da sauran wurare. Ya ce tunda har gwamnati ba ta ce masu komai kan sharuxxan da su ka gindaya mata ba, to sun fara yajin aikin kayan abincin har illa masha Allahu. Ya ƙara da cewa, “Akwai tasfos da mu ka kafa da zai aiwatar da umarnin da ƙungiya ta bayar cewa ba za a yi sufurin shanu da kayan abinci zuwa Kudu ba daga ranar Alhamis.

Saboda haka, ƙungiya ta kafa tasfos ɗin ne saboda maganin waɗanda za su yi mana zagon ƙasa. A takardar sanarwa da mu ka fitar, mun ce yajin aikin zai fara ne daga jiya, saboda haka mun fara yajin aikin. Daga yanzu babu sauran lodin kaya zuwa Kudu, amma duk waɗanda su ka nemi karya umarnin mu ne mu ka tare a Jihar Neja.”

Da alama dai cikin vacin rai ƙungiyar ta ɗauki wannan matakin. Babu shakka, tilas ne rai ya vaci ganin yadda ake kashe ‘yan Arewa a Kudu a kan dalilin da bai kai ya kawo ba. Daidai ne a nuna cewa ‘yan Arewa da ke Kudu ba daga sama su ka faɗo ba, su na da gatan su. Amma shin matakin hana kai kayan abinci ne kaɗai makamin da ya kamata Arewa ta yi amfani da shi don nuna rashin amincewar ta?

Na farko dai, da gaske ne cewa matakin ya jawo ƙarancin kayan abincin a sassan Kudu. Mun ji yadda nama ya yi tsada, domin bajimin da ake sayarwa a kan N150,000 ya koma N250,000, ta yadda duk mahaucin da ya yi yanka a haka, to zai gamu da asara; farashin kwandon tumatir ya yi tashin gwauron zabo daga N15,000 zuwa N38,000. Yaji kuwa, wanda muhimmin sinadari ne a abincin Yarabawa, ya zama ɗan gwal. Idon maciya ‘suya’ ya fara raina fata. Babu shakka, kowa ya ji a jikin sa. Haka AUFCDN ta ke so!

Amma hakan ya dace? A nawa ra’ayin, duk matakin da aka ɗauka a cikin fushi da hanzari ba zai haifar da ɗa mai ido ba. Shi ya sa matakin ya cutar da su kan su ‘yan kasuwar.

Burin ɗan kasuwa ne ya ci riba idan ya kai kaya kasuwa. To sai ga shi an hana shi kaiwa. Kayan nan kuma akasarin su masu sau