Trump da Harris sun kammala matakin ƙarshe na yaƙin neman zaɓe

Daga BELLO A. BABAJI

Ƴar takarar kujerar shugaban ƙasar Amurka, Kamala Harris ta gabatar da yaƙin neman zaɓe a karo na ƙarshe, kwanaki uku kafin zaɓen ƙasar.

Harris ta halarci wani shirin barƙonci ne na wani gidan telebijin a karon farko wanda an ɗauki shekaru da dama ana yi inda ƴan takarar shugaban ƙasa su kan shiga cikin shirin sakamakon shaharsa.

Haka ma Tsohon shugaban ƙasar kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, Donald Trump ya kammala nasa yaƙin neman zaɓen inda tuni aka fara hasashen sakamakon zaɓen.

A halin yanzu jihohi bakwai ne ake ganin fafatawa za ta yi ƙarfi tsakanin ƴan takarar biyu.

Wani sakamako da aka fitar a ranar Asabar ya nuna Harris a matsayin wacce ke kan gaba a yankin Lowa, wadda jiha ce da Trump ya yi nasara cikin sauƙi a zaɓuka biyu da aka yi a baya.

Trump ya ce matuƙar aka zaɓe shi, zai fitar da miliyoyin baƙin haure daga ƙasar tare da yin gargaɗin cewa matuƙar aka zaɓi Harris, to kowane birni a Amurka zai koma sansanin ƴan gudun hijira mai muni.

Ita kuwa abokiyar hamayyar tasa, cewa ta yi Trump zai ɓata ƙarfin ikonsa ne matuƙar ya zama shugaban ƙasa, ta na mai cewa mutum ne da a kullum ke ƙara rikicewa, wanda ke cikin fushi a halin neman ramuwa.