Shugaba Donald Trump ya ce, duk afuwar da tsohon shugaban ƙasar Joe Biden ya yi “ya tashi a banza” ne bayan da aka yi zargin cewa magabacinsa na jam’iyyar Democrat an yi amfani da na’ura ne wajen sanya hannu maimakon hannunsa.
Shugaban ya wallafa a shafinsa na Truth Social da sanyin safiyar Litinin, inda ya bayyana shakku kan sahihancin afuwar Biden, yana mai cewa ya yi amfani da na’ura wajen sanya hannu kan takardu maimakon yin hakan da hannu.
Ba tare da shaida ba, Trump ya yi iƙirarin cewa, Biden ya gaza bada hujja ga afuwar da ya yi ta hannun zaɓaɓɓun mambobin majalisar tara da suka binciki tashe tashen hankula a babban birnin Amurka a ranar 6 ga Janairu, 2021 tare da “da yawa” da aka wa afuwa a ranarsa ta ƙarshe kan karagar mulki, wato ranar 19 ga Janairu.
Trump ya rubuta cewa “‘Afuwar cikin Barci Joe Biden ya bai wa kwamitin da ba a zaɓa ba na ‘yan bangar siyasa, da sauran su da yawa, a nan an bayyana su a matsayin aikin banza, waɗanda ba su da ƙarfi ko tasiri, sakamakon tabbacin cewa, injin ne ya yi sa hannun a maimakon hannun tsohon shugaban. “
“Watau Joe Biden bai sanya hannu a kansu ba, asali ma bai san komai game da su ba! Ba a bayyana wa Biden takaddun da suka dace ba, ko amincewa da su.”
Shugabanni na iya ba da afuwa (cire hukunci bayan yanke hukuncin kotu) da ragi (raguwar hukuncin wani laifi) kamar yadda suka ga ya dace a matakin tarayya, amma ba da laifukan da suka shafi jihohi ba.