Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da lafta harajin kashi 25 kan ƙarafai da samfolon ko kuma Alminium da ake shigarwa ƙasar daga ƙetare ba tare da cirewa ko kuma sauƙaƙawa kowacce ƙasa ba.
Harajin na Trump kan ƙarafa da Alminium ko kuma Samfolon da ake shigarwa Amurka da zai fara aiki nan take, duk da cewa kai-tsaye shugaban Chana ya nufata da shi amma zai fi illa ga ƙasashen Canada da Brazil da kuma Meɗico waɗanda sune suka fi shigar da kayan cikin Washington.
A jawabinsa bayan sanar da lafta harajin, Trump ya bayyana cewa wannan muhimmin lamari ne kuma abu ne mai kyau, domin Amurka za ta sake samun maƙuden kuɗaɗe.
Cikin jerin ƙasashe 10 mafiya shigar da ƙarfe Amurka, Chana ke matsayin ta ƙarshe da kashi sufuri da ɗigo 51 na yawan ƙarafa da Samfolo ko Alminium da Amurkan ke buƙata, wannan kuwa baya rasa nasaba da harajin da Trump ya lafta mata tun a wa’adinsa na farko aka kuma ci gaba da aiwatar da shi har a wa’adin Joe Biden, lamarin da ya tialsta Beijing karkatar da kasuwarta zuwa wasu sassa.
A gefe guda Amurka ta koma sayen ƙarafa da Alminium daga wasu ƙasashen musamman maƙwabtanta saboda ƙarancin masu shigo da ƙarfen daga Chana.
Sai dai wasu bayanai sun ce, har zuwa yanzu galibin ƙarafan da ake shigarwa Amurka na fitowa ne daga Chana, domin Beijing a matsayinta na babbar mai samar da ƙarafa a duniya, ta kan sayar da su ne ga wasu ƙasashe su kuma su shigar da su Washington a matsayin nasu, kasancewar ba su da haraji mai tsauri.
Canada ce ƙasa mafi shigar da ƙarafa da Alminium Amurka da kashi 6.56 biye da Brazil da kashi 4.50 sannan Meɗico da kashi 3.52, akwai Korea ta Kudu da kashi 2.81 sannan ɓietnam da kashi 1.36.
Sauran ƙasashen sun ƙunshi Japan da kashi 1.18 sannan Jamus da kashi 1.07 sai Taiwan da kashi 1.01 tukuna Netherlands da kashi 0.61 sai kuma Chana a ƙarshe da kashi 0.51. RFI