Trump ya lashi takobin ƙara haraji kan Mexico, Kanada da Chana

Zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald Trump mai jiran gado ya ce, zai sanya haraji mai yawa kan duk wasu kayayyaki daga Mexico da Canada da kuma ƙarin haraji kan kayayyakin da Chana ke shigowa da su da zarar ya koma fadar White House.

Trump ya bayyana hakan ne a shafinsa na sada zumunta na Truth Social, wanda yake mallakin shi. Inda ya ƙara da cewa, zai sanya hannu kan dokar zartar da hakan a ranar farko da ya hau kan karagar mulki.

A cewarsa, jadawalin kuɗin fita zai ci gaba da kasancewa har sai lokacin da muggan ƙwayoyi, musamman Fentanyl, da duk wasu Baƙi ba bisa ƙa’ida ba za su ƙaura daga ƙasarmu.

“A ranar 20 ga watan Janairu, a jerin umurni na farko da zan zartarwa, zan sanya hannu kan duk takaddun da suka wajaba don cajin Mexico da Kanada harajin kashi 25 cikin 100 kan duk kayayyakin da ke shigowa Amurka, da kuma buɗe iyakokinta.

“Duk da cewa dukkan Mexico da Kanada suna da cikakken ‘yanci da ikon magance wannan matsala mai daɗewa cikin sauki,” inji Trump.

“Don haka muna buƙatar su yi amfani da wannan ƙarfin don kawo ƙarfen matsala, amma kuma har zuwa lokacin da za su yi hakan, za su biya faraji mai yawa,” inji shi.

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya kuma ce, za a ƙara harajin kashi 10 cikin 100 kan kayayyakin da ake shigo da su daga ƙasar Sin har sai an daina kwararowar magunguna a ƙasarmu, galibi ta hanyar Mexico.