Trump ya rushe sashen binciken kuɗaɗen da Abacha ya ɓoye

Daga USMAN KAROFI

Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya rusa wani sashi na musamman a Ma’aikatar Shari’a ta ƙasar (DOJ) da ke bin diddigin kadarorin da aka ɓoye daga Najeriya, ciki har da kuɗaɗen da tsohon shugaban mulkin soja, Janar Sani Abacha, ya ajiye. Wannan sashe mai suna “Kleptocracy Asset Recovery Initiative” an kafa shi ne a shekarar 2010, domin gano kadarorin da aka ɗauka daga ƙasashe daban-daban.

Wani majiya daga cikin ƙungiyar ya bayyana cewa sabon Antoni Janar na Amurka, Pam Bondi, ya rushe wannan sashi a makon nan, bayan samun umarnin daga Shugaba Trump. Wannan mataki ya zo a ba-zata, ganin cewa sashin ya taka rawa wajen gano da kuma dawo da biliyoyin daloli, ciki har da kuɗaɗen da ke da nasaba da Atiku Bagudu, ministan kasafin kuɗin Shugaba Bola Tinubu.

Rushe wannan sashi na iya kawo cikas ga ƙoƙarin gano sauran kuɗaɗen Abacha da ba a gano ba, waɗanda jami’an bincike ke zaton har yanzu suna ɓoye a wasu wurare. Haka nan, babu cikakken bayani kan yadda za a ci gaba da shari’o’in da ke kotunan Amurka da kuma haɗin gwiwa da sauran ƙasashe kamar Birtaniya wajen dawo da waɗannan kuɗaɗen.

Gwamnatin Trump ta bayyana cewa za ta fi mai da hankali kan yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi da na bil’adama, maimakon binciken kadarorin da aka wawure daga ƙasashe daban-daban. A halin yanzu dai, babu martani daga hukumar EFCC ko kuma mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, game da wannan mataki na gwamnatin Amurka.